Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Wakilin Al-Mayadeen a Zirin Gaza, ya ba da labarin shahadar mutane 8 da jikkatar mutane 26 sakamakon Hare-Haren Isra'ila kan Zirin Gaza tun sanyin safiyar yau Asabar.
Wakilin ya kuma yi nuni da shahadar wani mutum sakamakon raunin da ya samu kwanaki da suka gabata daga harsashin mamayar a Deir al-Balah a tsakiyar Zirin.
"Yawancin asibitocin Gaza suna fuskantar lalacewa, kuma suna buƙatar sake gyarawa da kuma samar musu da duk na'urori da kayan aikin likita da sojin Isra'ila suka lalata a lokacin da suka shiga yawancin waɗannan asibitocin kuma suka dakatar da su daga aiki."
A cikin ci gaba da hare-haren mamayar, wakilin Al-Mayadeen a Gaza ya ba da labarin raunata wata yarinya da harsashin mamayar a cikin tantinta a Wadi al-Salqa a kudancin Deir al-Balah a tsakiyar Zirin.
Ya kuma yi nuni da shahadar wani ɗan ƙasa sakamakon harin Isra'ila kusa da zagayen Abbas al-Kilani a Beit Lahia a arewacin Zirin Gaza.
A gaba nin hakan a yau Asabar, ma'aikatar lafiya a Gaza ta bayyana cewa adadin shahidai da waɗanda suka ji rauni tun a ranar 11 ga Oktoba 2025 har zuwa yau ya ƙaru zuwa shahidai 1,445 da jikkatar 5,072, yayin da ayyukan ciro gawa suka kai shahidai 835.
Ma'aikatar ta kuma tabbatar da cewa jimillar ƙididdiga tun farkon mamayar ta kai shahidai 74,228 da raunatar 175,188.
Wannan yana zuwa ne a cikin tsarin kammala kisan kare dangi na mamayar a Zirin, ta hanyar kai hari kan fararen hula marasa tsaro, daga yara da mata, da kai hari kan tanti da gidaje da hanyoyi, da lalata ababen more rayuwa da kayan rayuwa, tana mai keta yarjejeniyar "dakatar da wuta" da aka sanar.
……………
Ra'ayinka